Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an hukumar zabe 30 sun bace yayin zabukan Kogi da Bayelsa

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce jami’anta 30 sun bace, yayinda suke tsaka da aikin tattara sakamakon kuri’un da aka kada a zaben gwamnan jihar Kogi.

Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya yayin tantance masu kada kuri'a.
Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya yayin tantance masu kada kuri'a. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

INEC tace dukkanin jami’an an tura su ne karamar hukumar Olamaboro, wadanda da misalign karfe 1 na daren jiya hukumar ta yi shelar bacewarsu.

Bangarori daban daban dai na ci gaba da yin tsokaci kan zabukan gwamnan jihohin Kogi da Bayelsa da suka gudana a jiya asabar, wadanda a dukkanin jihohin aka fuskanci tashe-tashen hankula yayin kada kuri’a, satar akwati da kuma sayen kuri’ar, duk da wanzuwar dubban jami’an tsaron da aka girke.

A Bayelsa inda ake fafatawa tsakanin yan takara 45 ciki har da dan takarar PDP Douye Diri da Mista David Lyon na jam’iyyar APC, an soke kuri’un da aka kada a wasu rumfunan zabe musamman a yankin Ogbia, saboda tashin hankalin da ya kai ga sace jami’in zabe, akwatunan zaben da kuma, kone kuri’u.

Kan tashe-tashen hankulan ne kuma gwamnan jihar ta Bayelsa Seriake Dickson ya zargi jami’an tsaro da baiwa ‘yan bangar siyasa damar cin karensu babu babbaka.

A jihar Kogi kuwa inda Gwamna Yahya Bello ke neman wa’adi na biyu, yana fafatawa ne da MusaWada na jam’iyyar PDP gami da wasu ‘yan takara 22, kwamishin ‘yan sandan jihar Hakeem Busari, ya ce gungun ‘yan bindiga da suka yi awon gaba da akwatunan zabe a wasu sassan jihar sanye da kayan jami’an tsaro, na bogi ne.

Tuni dai masu sa ido kan zaben Gwamnan na kogi, suka koka bisa tashe-tashen hankula, satar akwati, kaiwa ‘yan jaridu da jami’an sa ido farmaki da kuma sayen kuri’un da suka mamaye zaben, duk da wanzuwar jami’an tsaro akalla dubu 35 a jihar, kamar yadda a jiya rundunar ‘yan sandan kasar ta tabbatar.

Sai dai rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta hannun kakakinta Franka Mba, ta musanta gazawa wajen tabbatar da doka da oda yayin zabukan jihohin biyu, inda tace ta iyaka bakin kokarinta wajen samar da tsaro.

Ita kuwa hukumar zaben Najeriya INEC cikin wata sanarwa data fitar, ta ce mafi akasarin wadanda suka cancanta sun kada kuri’unsu yayin zabukan kujerun gwamnan a jihohin na Kogi da Bayelsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.