'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara
Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane akalla 18 a kauyen Karaye da ke Karamar Hukumar Gummi ta jihar Zamfara da ke Najeriya kamar yadda hukumomi da mazauna yankin suka tabbatar.
Wallafawa ranar:
Mazauana yankin sun bayyana harin a matsayin mafi muni da suka gani a cikin watannin baya-bayan nan, inda ‘yan bindigar suka kwashe tsawon sa’o’i hudu suna cin karansu babu babbaka ba tare da halartar jami’an tsaro ba.
Gwamnatin jihar ta bayyana harin a matsayin na ramuwar gayya sakamakon kisan da aka yi wa wasu daga cikin dangin ‘yan bindigar makwanni da suka shude a gunzumar Bardoki da ke Gummi.
A ranar 3 ga watan Nuwamba ne, ‘yan kato da gora suka kashe ‘yan bindga bakwai da suka tuba kamar yadda rahotanni ke cewa.
Jihar Zamfara ta yi fama da hare-haren ‘yan bindiga da suka kashe daruruwan mutane, yayin da Gwamnan Jihar, Bello Matawalle ya cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da ‘yan bindigar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu