Isa ga babban shafi
Najeriya

Tashin hankali ya mamaye kaso 60 cikin 100 na zaben gwamnoni - Rahoto

Masu sa ido a zaben da aka yi a Jihohin Kogi da Bayelsa dake Najeriya, sun bayyana damuwa kan irin tashin hankalin da suka gani da kuma gazawar jami’an tsaro wajen kare lafiyar masu kada kuri’u.

Wasu dake zanga-zangar rashin isowar kayayyakin zabe a Najeriya.
Wasu dake zanga-zangar rashin isowar kayayyakin zabe a Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Saboda haka ne suka bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tashi tsaye wajen ceto dimokiradiyar kasar daga durkushewa.

Bangarori daban daban dai na ci gaba da yin tsokaci kan zabukan jihohin na Kogi da Bayelsa, wadanda a dukkanin jihohin aka fuskanci tashe-tashen hankula yayin kada kuri’a, satar akwati da kuma sayen kuri’ar, duk da wanzuwar dubban jami’an tsaron da aka girke.

Idayat Hassan jagora ce ta jami’an da suka bi kwakkwafin abinda ya wakana yayin zabukan kujerun gwamnan, wanda yayin zantawa da wakilin sashin Hausa na RFI Muhammad Kabir Yusuf, ta ce bincikensu ya nuna cewar, tashe-tashen hankula sun mamaye akalla kaso 66 cikin 100 na rahotannin matsalolin tsaron da a bayyana ba. Zalika an baiwa ‘yan bindiga damar cin karensu ba babbaka.

Domin sauraron cikakken bayanin jami’an sa ido kan zabukan gwamnonin na Bayelsa da Kogi sai a latsa alamar sautin dake kasa domin jin rahoton wakilinmu Muhammadu Kabiru Yusuf.

01:41

Tashin hankali ya mamaye kaso 60 na zaben gwamnoni - Rahoto

Kabir Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.