Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun ceto mata da yara daga hannun Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya ta ce, dakarunta sun yi nasarar cafke wasu mayakan Boko Haram, yayin da suka kubutar da mata da kananan yara 165 daga hannun mayakan a jihar Borno.

Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram AP/Lekan Oyekanmi
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis a birnin Abuja ta bakin jami’inta da ke kula da kafafen yada labarai, Kanar Aminu Iliyasu, rundunar ta ce, an kaddamar da samame kan mayakan ne tare da hadin guiwar dakarun kasa da kasa.

Kanar Iliyasu ya ce, tuni suka mika kananan yaran ga jami’an kiwoan lafiya domin yi musu allurar riga-kafin kamuwa da cutar Polio.

Jami’in ya kara da cewa, sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Buba wanda ya kware wajen kwarmata wa kungiyar Boko Haram bayanan sirri, yayin da kuma suka kwace wasu makamai da suka hada da kibiyoyi daga hannun mayakan.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin kasar ta bayyana shirinta na janye dakarunta daga wasu yankuna na Najeriya da suka hada da arewa maso gabashin kasar domin maye gurbinsu da ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence, matakin da tuni ya haddasa cece-kuce a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.