Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari yayi karin bayani kan shirin janye sojoji daga sassan kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci kwantar da hankula dangane da shirin gwamnatinsa na janye dakarun kasar daga wasu yankuna, ciki harda yankin arewa maso gabashi mai fama da rikicin Boko Haram.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP
Talla

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, 3 ga Janairun 2020, lokacin da yake karin bayanin cewar, za a janye dakarun sojin kasar ne da kuma maye gurbinsu da ‘yan sanda la’akari da cewar Najeriya bata cikin hali na Yaki.

Cikin sanarwar da shugaban Najeriyar ya fitar ta hannun kakakinsa Garba Shehu, ya ce lokaci yayi da a yanzu sojoji za su maida hankali wajen ainahin aikinsu na kare kasar daga duk wata barazana daga ketare.

A bangaren yankunan masu fama da matsalolin tsaro na cikin gida kuma, za a maye gurbin sojojin da hadin gwiwar rundunonin ‘Yan sanda da Civil Defence, idan lokacin soma aiwatar da shirin yayi.

Sai dai duk da cewa shugaban ya ce ba za a yi gaggawa wajen soma aiwatar da shirin ba, tuni wasu gwamnonin jihohin kasar musamman wadanda abin ya shafa, gami da sauran jagororin al’umma suka bukaci janye wannan aniya, saboda hadarin dake tattare da ita.

Kafin gabatar da koken dai shugaba Buhari yace za a baiwa masana tsaro damar yin cikakken nazari kan matakin, kafin soma aiwatar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.