Isa ga babban shafi
Najeriya

Sakamakon wasu zabukan cike gurabe a jihohin Najeriya

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana sakamakon wasu daga cikin zabukan cike gurbin ‘yan majalisu a matakan tarayya da na jihar da aka yi a jihohin kasar 11, a ranar asabar.

Wani jami'in hukumar zaben Najeriya.
Wani jami'in hukumar zaben Najeriya. REUTERS/Adelaja Temilade
Talla

A Kaduna hukumar zaben ta bayyana Nuhu Shadaliya na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin dan majalisa na mazabar Kagarko da kuri’u dubu 24 da 658, inda ya doke Tanko Monrondia na PDP da ya samu kuri’u dubu 20 da 206.

A karamar hukumar Sanga kuwa Mrs Comfort Amwe ta PDP ce ta lashe zaben da kuri’u dubu 19 da 815, inda ta doke Halliru Gambo na APC daya samu kuri’u dubu 19 da 688.

A bauchi dan takarar PDP Auwal Jatau ne ya lashe zaben cike gurbin dan majalisar tarayya na mazabar zaki da kuri’u dubu 15 da 405, yayinda Tata Umar na APC ya samu kuri’u dubu 15 da 307.

A kano Ali Datti Yako na PDP ya lashe kujerar majalisar wakilai ta Kiru da Bebeji bayan samun kuri’u dubu 48, da 601, inda ya doke Abdulmumin Jibril Kofa na APCma kuri’u dubu 13 da 507.

A jihar Imo, Mrs Miriam Onuoha ta APC ce ta lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta mazabar Okigwe ta Arewa da kuri’u dubu 23 da 690, inda ta doke Obinna Onwubuariri na PDP mai kuri’u dubu 10, da 10.

A Cross River kuwa, Mr Alex Egbona na APC ne ya lashe zaben dan majalisar wakilai na mazabar Abi da Yakurr, da kuri’u dubu 29 da 716, inda ya doke John Gaul na PDP mai kuri’u dubu 26, da 39.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.