Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Koli za ta sake sauraron kararrakin zabukan Imo da Bayelsa

Kotun kolin Najeriya ta sanya ranar talata mai zuwa a matsayin ranar da zata saurari daukaka karar da tsohon Gwamnan Jihar Imo Emeka Ihedioha ya shigar tare da karar da David Lyon na Jihar Bayelsa ya gabatar mata.

Kotun Kolin Najeriya.
Kotun Kolin Najeriya. Daily Post
Talla

Mai Magana da yawun kotun, Festus Akande ya tabbatar da shirin zaman kotun kamar yadda aka gabatar da kara daga bangarorin biyu.

Ihedioha na Jam’iyyar PDP na bukatar kotun ta sake nazari kan hukuncin da ta yanke wanda ya raba shi da mukamin sa, ya kuma baiwa Jam’iyyar APC mulkin Jihar ta Imo bayan an rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayun bara.

Shima David Lyon ya gabatar da irin wannan kara a kotun ne inda yake kalubalantar hukuncin da ta yanke ranar alhamis, kwana guda kafin rantsar da shi, inda ta soke zaben sa saboda samun mataimakin sa da gabatar da takardun bogi ga hukumar zabe.

Wannan hukuncin ya sa hukumar zabe gabatar da takardar shaidar samun nasara ga Sanata Douye Diri na Jam’iyyar PDP wanda aka rantsar jiya juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.