Isa ga babban shafi
Najeriya

'Buhari ba zai yi murabus ba saboda matsalar tsaro'

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce, shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi murabus ba saboda tabarbarewar tsaro a sassan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter/Asorock
Talla

Ministan Yada Labarai da Al’adu na kasar, Lai Mohammed ya fadi haka a birnin Abuja a daidai lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis.

Ministan ya mayar da martani ga masu kiraye-kirayen shugaba Buhari da ya sauka daga kujerarsa saboda gazawarsa wajen tabbatar da tsaro a cewarsu.

Ko a baya-bayan nan, Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya, Eyinnaya Abaribe ya bukaci shugaba Buhari da ya yi murabus saboda wannan matsalar ta rashin tsaro a kasar.

Najeriya na fama da rikicin Boko Haram da matsalar sace-sacen mutane don karbar kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga da ke kashe mutane babu kakkautawa a wasu jihohin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.