Isa ga babban shafi
Najeriya

Kwalejin Adamawa za ta kori malamanta

Babbar Kwalejin Fasaha ta Jihar Adamawa da ke Najeriya na shirin korar hudu daga cikin manyan malamanta saboda samun su da laifin sauya sakamakon jarabawa da kuma bai wa daliban da ba suyi jarabawa ba maki.

Dakin rubuta jarrabawa a Najeriya
Dakin rubuta jarrabawa a Najeriya Buzznigeria
Talla

Jami’in Hulda da Jama’a na makarantar, Albert Matilah ya shaida wa manema labarai cewar, shugabannin gudanarwar makarantar sun amince da rahoton binciken da aka yi kan lamarin, wanda ya bada shawarar daukar matakin korar su daga aiki.

Sanarwar ta bayyana malaman guda hudu da suka hada da Abubakar Babale da Paul Wache da Usman Hammawarbi da kuma Isa Ribadu.

Matilah ya ce, Babale wanda shi ne shugaban sashen koyar da aikin jarida ya sauya sakamakon jarabawa 727, yayin da Wache wanda shi ne shugaban sashen koyar da kimiyar kasa ya sauya sakamakon jarabawa 83 a kwasa-kwasai 12, kuma ya bayyana cewar kuskure ya sa shi yin haka.

Jami’in ya c,e an kuma samu Wache da laifin bayar da sakamakon bogi ga dalibin da bai yi jarabawar ba, kamar yadda malamin da ke koyar da wannan kwas ya tabbatar.

Shi kuwa Usman Hammarwabi an same shi ne da laifuffukan sauya sakamakon jarabawa da kyautar maki ga dalibai da kuma wasu laifuffuka na daban, yayin da aka samu Isa Ribadu da irin wadannan laifuffuka.

Kwamitin binciken da aka kafa ya bai wa malaman damar kare kan su kuma sun amsa laifin da suka yi.

Matilah ya shaida wa RFI Hausa cewar, yanzu haka hukumar gudanarwar makarantar ta mika rahotan ga ma’aikatar ilimin Jihar Adamawa domin aiwatar da hukunci saboda a halin yanzu, makarantar ba ta da shugabannin majalisar gudanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.