rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Niamey

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jamian Tsaro a Kasar Niger na tsare da mutane 76 saboda boren Dalibai

media
Shugaban Nijar Muhammadu Isufu AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA

A kasar Janhuriyar Nijar ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Gwamnati da dalibai na makarantu  gameda batun da suke neman na inganta  harkan ilmin a makarantun su.


Wannan bukata ta daliban ta haifar da zanga-zangan dalibai a Yammai inda mutane bakwai suka sami raunuka.

‘Yan sanda sun bayyana cewa suna tsare da mutane 76 saboda hannun wajen zanga-zangan.

Mun nemi ji daga bakin Dr Maina Bukar malami a jamiar Yammai yadda take kallon wannan bore na dalibai