rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Muhallinka Rayuwarka
rss itunes

Itacen Dakwara na yaki da kwararowar hamada

Daga Awwal Ahmad Janyau

Shirin Muhallinka Rayuwarka ya mayar da hankali ne a Jamhuriyyar Nijar game da muhimmacin iccen Dakwara wajen kare gurgusowar Hamada da kuma wasu alfanun iccen ga kasar noma.

Daya daga abinda ke kare hamada ta hanyar rage gusowar rairai tare da iska sannan da raya kasar noman da ta sallace, Masana na ganin babu kamar iccen Dakwara wanda ke fitar da Karo.

Tun shekara ta 2003 gwamnatin shugaba Tandja Mahamadu ta fito da wani sabon tsari na bunkasa noma wannan icce a fadin kasar.

Wannan kuma don yaki da gurgusowar hamada sannan da samar da kudin shiga ga manoma lura da irin makudan kudaden karo da manoman kasashen Sudan da Tchadi ke samu, abin da ya sa suka fita sha’anin noma suka mayar da hankali ga iccen na dakwara.

Sai dai shekaru 13 bayan wannan hobbasa da dama daga manoman Dakwara sun yi watsi da wannan sana’a saboda rashin samun biyan bukata bayan sun shuka ekoki da Dama.

Shirin ya tattauna da manoman Iccen da kuma masana kan yadda za a farfado da noman shi da kuma matakan samuun Karo.

Kalubalen da rikicin Zamfara zai haifarwa fannin Noma a Najeriya

Yadda rikicin Zamfara ke shirin haddasa kamfar abinci a Najeriya

Rashin tsaro ya tilastawa wasu makiyayan Najeriya da Nijar tserewa zuwa Chadi

Manoma na tafka asarar kashi 30 cikin 100 na hatsin da suke nomawa a shekara

Dalilan da suke haddasa tsadar kayan abinci a Najeriya duk da karuwar wadanda ke rungumar noma

Yadda ambaliyar ruwa ta yi banna a wasu sassa na Arewacin Najeriya

Rabuwar kawuna dangane da amfani da wasu nau'uka na takin zamani

Matakin Najeriya na ganin an farfado da tafkin Chadi don samar da aikin yi

Cutukan da ke barazana ga dabbobi da amfanin gona tare da hanyoyin magance su

Dalilai na kimiyya da ke haddasa guguwa mai dauke da kakkarfan ruwan sama.

Leda na haifar da illoli ga muhalli da lafiyar dan adam - Masana