rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Ta'addanci Mahamadou Issoufou

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Nijar ya bukaci goyon baya don yakar ta'addanci

media
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou. BOUREIMA HAMA / AFP

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ya ce akwai bukatar al’ummar kasar baki daya su tashi tsaye haikan domin tunkarar barazanar ayyukan ta’addanci da kasar ke fuskanta daga makotanta.


Shugaba Issoufou wanda ke gabatar da jawabi lokacin wani taro da ya hada illahirin shugabannin kananan hukumomin kasar a birnin Yamai, ya bayaar da misali yadda 'yan ta’addar ke yawan kai wa kasar hare-hare a kan iyakokinta da Mali da Najeriya da kuma Chadi.

Yanzu haka dai an kafa dokar ta baci cikin wasu johohi uku wato Tillaberi, Tawa da kuma Diffa sakamakon hare-hare daga 'yan ta'adda.