rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Karancin Abinci Rahotanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Karancin Abinci ya mamaye Nijar

media
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou. BOUREIMA HAMA / AFP

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da samun karancin abinci a wasu sassan kasar, sakamakon rashin damuna mai kyau a shekarar da ta gabata.


Ministan cikin gida Bazum Muhammed ya ce bayan farin da aka samu, yanzu haka kasar na bukatar irin shuka da ya kai ton 15 da za’ayi amfani da shi a wannan shekara.

Jihohin Damagaran da Zinder da Tahoua da Tilebiri na daga cikin inda rashin abinci ya yi kamari, kamar yadda Alhaji Umar Isa wani manomi a Damagaran ya shaidawa RFI.

Cikakkiyar hirar Alhaji Umar Isa da RFI.

Akwai karancin abinci a Nijar 10/05/2017 - Daga Umaymah Sani Abdulmumin Saurare