rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Zaben Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar Dokokin Nijar ta amince da yiwa tsarin zabe gyaran fuska

media
Ginin majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar. Alamy

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da a aiwatar da wasu gyare-gyare a kundin tsarin mulkin kasar, wanda zasu shafi muhimman al’amuran kasar ciki harda tsarin gudanar da zabe.


A karkashin gyare-gyaren, za’a gudanar da zaben shugabancin kasar zagaye na farko, kwanaki 120 kafin karewar wa’adin shugaban da ke kan karagar mulki, a maimakon kwanaki 40, kamar yadda tsarin yake a baya.

Ministan cikin gidan kasar Bazum Mohammed wanda ya wakilci gwamnati a gaban majalisar kasar, ya shaidawa RFI Hausa cewa hakan zai bai wa kotu isasshen lokaci na sauraron karar da duk wata jam’iyya ta gabatar mata, bayan kammala zabe kafin kama aikin sabuwar gwamnati.

Majalisar Nijar ta amince da yiwa tsarin zabe gyaran fuska 30/05/2017 - Daga Nura Ado Suleiman Saurare