Isa ga babban shafi
Nijar

Matan Nijar sun bukaci daukan mataki kan Boko Haram

A garin Nguimi da ke Diffa a jamhuriyar Nijar, daruruwan mata ne suka yi kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakan da suka wajaba domin ceto mutane 39 da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace a garin Ngalewa da ke yankin tun farkon wannan wata har har yanzu babu duriyarsu.

Jama'ar yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar na cikin fargaba saboda barazanar mayakan Boko Haram
Jama'ar yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar na cikin fargaba saboda barazanar mayakan Boko Haram irinnews.org
Talla

Mutanen da Boko Haram ta sace tun ranar 2 ga watan Yulin da ya gabata, sun hada da mata 33 da kuma ‘yan mata guda 6.

Lura da cewa ‘yan Boko Haram na kai wa jama’a hari ne mafi yawan lokuta a cikin dare, wannan ya sa wasu ke ganin cewa lokaci ya yi da ya kamata a bai wa jama’a damar kafa kungiyoyin matasa domin kare kai daga mahara.

Alhaji Gremah Bukar, daya daga cikin shugabannin al’umma a yankin Maini da ke jihar ta Diffa , ya ce ba su da ‘yan kato da gora irin na Najeriya da ke taimaka wa wajen samar da tsaron jama’a.

Alhaji Bukar ya bada misali da garin Malam-bulamari da ya samu kwanciyar hankali saboda matakin da ya dauka na kafa jami’an tsaro na sa kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.