Isa ga babban shafi
Nijar

Gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da tsawaita dokar ta bacin da ta kaddamar a yankin Diffa saboda ci gaba da barazanar tsaron da ake fuskanta a yankin.

Daya daga cikin jami'an sojin Jamhuriyar Nijar a lokacin da yake gadin 'yan gudun hijira a yankin Diffa, da ke kudu maso gabashin kasar.
Daya daga cikin jami'an sojin Jamhuriyar Nijar a lokacin da yake gadin 'yan gudun hijira a yankin Diffa, da ke kudu maso gabashin kasar. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Sanarwar gwamnatin ya nuna cewar an tsawaita dokar ne daga yau 18 ga watan Satumba zuwa watanni 3 nan gaba.

Zalika tawaita dokar ya shafi yankin dake makwabtaka da Mali inda ake samun hare hare a Tilaberi da Tawha.

To sai dai a nasu bangaren wasu daga cikin mazauna yankunan da matakin ya shafa sun ce zai yi wahala matakin tsawaita dokar ta bacin ya yi tasiri wajen magance barazanar tsaron, kamar yadda wani mazauni a yankin na Diffa AbdouSalam Djamal ya shaidawa sashin Hausa na RFI.

00:30

Gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.