rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kwashe wasu bakin haure 25 daga Libya

media
Wasu bakin haure da aka kwashe daga Libya REUTERS/Hani Amara

Majalisar dinkin Duniya tayi nasarar kwashe wasu bakin haure 25 daga Libya zuwa Nijar domin tsugunar da su.


Matakin wani yunkuri ne na kare lafiyar bakin wadanda ke fadawa cikin tahsin hankali sakamakon hare hare da kuma garkuwar da akeyi da wasu daga cikin su domin karbar kudi.

Hukumar kula da Yan gudun hijira ta Majalisar tace yanzu haka baki da dama na tsare a hannun kungiyoyin dake dauke da makamai, inda ake azabtar da su da kuma yiwa wasu daga cikin su fyade.

Hukumar ta ce yanzu haka baki 43,000 suka yi rajista da ita a Libya.