rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Mahamadou Issoufou

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nijar na bikin cika shekaru 59 da zama Jamhuriya

media
Shugaban Jamhuriyar Nijar Issifou Mahamadou ONEP-NIGER

A wannan Litinin ake gudanar da bukukuwan cika shekaru 59 da kasancewar Nijar, kasa kuma Jamhuriyar.


A wannan karon birnin Tawa ne ke karbar nauyin gudanar bikin.

A lokacin wannan bikin ne shugaban kasa Issifou Mahamadou zai kaddamar da ayyuka da dama da aka gudanar, domin raya wannan birni, da suka hada da hanyoyi, gidaje, filin sauka da tashin jiragen sama da dai sauransu.

Shugabannin kasashen Afirka 6 ne ake kyautata zaton cewa za su halarci wannan biki da suka hada na Najeriya Muhammadu Buhari, da takwarorinsa na Burkina Faso, Chadi, Mali da kuma Mauritaniya.

A kowace shekara hukumomin Nijar na zabar jihar da zata za’a karbi bakuncin gudanar da bikin.