Faransa za ta taimaka wa Nijar wajen kafa sabuwar gwamnati
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce babban aikin da ke gaban shugaban Nijar Mahammadou Issofou a halin yanzu shi ne gudanar da karɓaɓɓen zaɓe a shekara ta 2021.
Wallafawa ranar:
Macron wanda ya zanta da shugaban na Nijar a cigaban ziyarar da yake yi a ƙasar, ya ce gwamnatinsa za ta taimaka wa Nijar wajen tabbatuwar hakan ta hanyar inganta zaɓuka masu zuwa.
Ya ƙara da cewa ƙasar ta Nijar ba za ta ci gaba ba, matuƙar ba ta samar da tsaro da kuma ingantaccen tsari na mulkin demokraɗiyya ba.
Zaben shekara ta 2021 da ake sa ran gudanarwa a ƙasar zai kasance zakaran-gwajin-dafi, kasancewar ƙasar ba ta taɓa samun nasarar miƙa mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata ta farar hular ba.
Sauran ɓangarorin da Faransa din za ta taimaka wa Nijar sun haɗa da inganta tsaro da kuma ci gaban ƙasa, a cewar Macron.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu