rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Sahel Ta'addanci Emmanuel Macron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zamu tsananta yakar ta’addanci a yankin Sahel cikin 2018 - Macron

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayinda ganawa da dakarun kasarsa a birnin Yamai. LUDOVIC MARIN / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ke ziyara a Jamhuriyar Nijar da nufin karfafa gwiwar dakarunsa da ke yakar ta'addanci, ya sha alwashin kara tsananta yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel cikin shekara mai kamawa ta 2018.


Faransa ce dai ke jagorancin yakin da ake yi da ta’addanci a yankin Sahel na yammacin Africa , inda a yanzu da ke da dakaru akalla 4000.

Zalika a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, akwai dakarun Faransa 500, da kuma jiragen yaki, da marasa matuki a cibiyar da kasar ta Faransa ta kafa, domin tallafawa wajen yakar ‘yan ta’adda.

A jiya Juma’a Macron ya isa Jamhuriyar ta Nijar, kuma wani lokaci a yau Asabar, zai gana da shugaban kasar Muhd Issofou. Bayan ganawar ce kuma ake sa ran shugaban na Faransa ya zai bayyana wasu manyan shirye-shirye da kasarsa zata jagoranta, musamman kan ilimantar da yara mata.