rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yanke wa manyan sojoji hukuncin shekaru 15 a gidan yari

media
Shugaban kasar Nijar Mahamdou Issoufou. REUTERS/Afolabi Sotunde/Files TPX IMAGES OF THE DAY

Kotu a jamhuriyar Nijar ta yanke wa sojoji guda 9 da wani farar hula 1 hukuncin tsakanin shekaru 5 zuwa 15 a gidan yari bisa zargin su da kitsa juyin mulki domin tuntsurar da gwamnatin shugaba Muhammadu Issoufou a shekara ta 2015.


Cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin har da Janar Souleymane Salou, tsohon babban hafsa kuma wanda ake zargi da kitsa juyin mulkin shekarar 2010, da kuma Laftanar Ousmane Awal Hambaly, wanda aka kora daga aikin soji a shekarar 2012 sakamakon samun sa da laifin kitsa wani juyin mulkin.

A cewar mai gabatar da ƙara, an shirya kama shugaba Issoufou da kuma babban dogarinsa ne a lokacin da suka dawo daga garin Maradi a ranar 18 ga watan Disamba, ko kuma a kashe su, da zarar suka kawo turjiya.

A watan Disamba na shekara ta 2015 ne aka kama wasu sojoji guda 12 bayan da shugaba Issoufou ya yi zargin cewa an bankaɗo wani yunkuri na kifar da gwamnatinsa.