'Yan fashi da makami a sun mika makamansu ga gwamnatin Nijar
Wasu 'yan fashi da makami a Jihar Agadez dake Jamhuriyar Nijar sun mika wa gwamnati tarin makamai dake hannun su a karkashin wani shiri na yi musu afuwa.
Wallafawa ranar:
Bakin mika makaman ya gudana ne a karkashin jagorancin Ministan cikin gida na Jamhuriyar ta Nijar Bazoum Mohammed.
Wannan dai shi ne karo na uku cikin kasa da shekara guda, da 'yan fashi da makami suke mika makamai ga hukumomin kasar.
Makaman sun hada da manyan bindigogi masu sarrafa kansu, makaman roka da kuma alburusai masu tarin yawa.
Mutane sama da 30 ne suka mika makaman ga gwamnati, tare da shan alwashin cewa zasu bai wa jami'an tsaron kasar gudunmawa wajen tabbatar da doka da oda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu