Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

An Yi Zanga-Zanga Saboda Neman Gyara A Kasafin Kudade na Janhuriyar Nijar

Wallafawa ranar:

A Janhuriyar Nijar, a jiya lahadi dubban mutane  suka yi zanga-zanga a sassa daban daban na kasar, inda suke jaddada bukatar ganin an yi wa dokar kasafin kudin kasar gyara, saboda a cewarsu dokar na tattare da karin haraji akan jama’a, kayayyakin abinci da dai sauransu.Har ila yau masu zanga-zangar wadda kungiyoyin fararen hula ne suka yi da aka gudanar da ita, na fatan ganin an janye sojojin kasashen ketare da aka jibge da yakar ayyukan ta’addanci a kasar.To sai dai ga alama gwamnatin Issoufou Mahamadou ba ta da niyyar saurarensu, inda a maimakon haka gwamnatin ta yi kira ga magoya bayanta da su fito domin yin zanga-zanga a ranar 4 ga wata gobe. Nouhou Abdou Magaji, mai sharhi ne kan lamurran yau da kullum a birnin Konni, ga abinda yake cewa dangane da wannan.

Shugaban Jamhuriyar Nijar  Issoufou Mahamadou
Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou rfi
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.