'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaron Nijar
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe jami’an tsaron jamhuriyar Nijar 3, tare da raunata guda daya, a kauyen Goube tazarar kilomita 40 da birnin Yamai fadar gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
Lamarin dai ya faru ne a cikin daren Litinin zuwa wayewar garin jiya Talata, inda rahotanni suka ce maharan sun zo ne a kan babura, kafin daga bisani su doshi bangaren iyakar kasar ta Nijar da Mali.
Wannan ne dai shi ne karo na farko da ‘yan bindiga ke kai hari makamancin haka a gaf da kofar birnin na Yamai, bayan irinsa da suka kai kusan shekaru 2 da suka gabata, a wani gidan yarin Koutoukale da ake tsare da ‘yan ta’adda a cikinsa.
Alkassoum Abdurrahman na daga cikin masana tsaro da ke kallon harin na baya bayan nan a mtsayin babbar barazana ga Jamhuriyar Nijar, kamar yadda ya bayyana a zantawarsa da Sashin Hausa na RFI.
Muryar Alkassoum AbduRahman masanin tsaro, akan hallaka jami'an tsaron Jamhuriyar Nijar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu