rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta bada umarnin bude gidan rediyon Nijar

media
Gwamnatin Nijar na zargin gidan rediyon da tinzira jama'a wajen bore Flickr/Curtis Kennington/CC/http://bit.ly/2mfKZKs

Wata Kotu a Jamhuriyar Nijar ta bada umurnin bude gidan rediyon Labari da gwamnati ta rufe a karshen mako saboda zargin cewar yana tinzira jama’a wajen tada hankali.


Alkalin kotun ya bayyana matakin rufe tashar a matsayin abin da ya saba ka’ida, in da ya bukaci jami’an tsaron da suke girke a tashar da su san in da dare ya yi musu.

Ali Idrissa, daya daga cikin shugabannin da suka shirya zanga zangar adawa da harajin gwamnati na can tsare a gidan yari tare da sauran abokan tafiyarsa.

Ministan cikin gida, Bazum Muhammed ya zargi tashar da zama bakin 'yan adawa wajen tinzira al’ummar kasar su yi mata bore.