rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nijar ta yi wa majalisar ministocinta garanbawul

media
Shugaban Nijar Muhamadou Issoufou ludovic MARIN / AFP

A Jamhuriyar Nijar an yi wa majalisar ministoci garambawul bayan da Ministan Harkokin Wajen kasar Ibrahim Yacouba ya yi marabus daga mukaminsa.


Sanarwar da kafafen yada labaran gwamnati suka fitar na cewa, tuni aka nada Kalla Hankurau a matsayin sabon Ministan Harkokin Waje, sai Mahamadou Salissou Habi a ma’aikatar sadarwa, yayin da aka nada Mohamed Samro a matsayin ma’aikatar ilmin sakandare.

Ga alama dai an tilasta wa Ministan Harkokin Wajen yin marabus ne, sakamakon yadda jam’iyyarsa ta fito fili ta bayyana rashin amincewa da sabuwar hukumar zaben da aka kafa a kasar.