Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan bindiga sun sace Bajamushe a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani baturen Jamus a yammacin kasar da ke kusa da iyaka da Mali.

'Yan bindiga sun ce baturen Jamus a garin Inetes da ke Ayorou na Jamhuriyr Nijar
'Yan bindiga sun ce baturen Jamus a garin Inetes da ke Ayorou na Jamhuriyr Nijar Reuters / Feisal Omar
Talla

Wanda aka sacen na aiki ne da wata kungiyar agaji mai suna Help, kuma lamarin ya faru ne kilomita 25 daga garin Inetes da ke Ayorou, yankin da ke karkashin dokar ta baci sakamakon matsalar tsaro.

Direban Bajamushen ya shaida wa hukumomin kasar cewa, ‘yan bindigar da suka iso kan babura sun tsare su ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga ziyarar da suka kai arewacin yankin.

Direban ya ce, ‘yan bindigar sun kuma lakada mu su dukan tare da kona motarsu kafin awon gaba da baturen.

Ko a cikn watan Oktoban bara, sai da aka kashe jami’an tsaron Nijar 12 a Ayorou.

Har ila yau a cikin watan ne aka kashe sojojin Amurka hudu da na Nijar hudu, abin da  gwamnatin kasar ta bayyana a matsayin ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.