rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Al'ummar Filingue sun koka bisa hare-haren 'yan bindiga

media
Wasu jami'an sojin Jamhuriyar Nijar. Reuters

A Jamhuriyar Nijar, shugabannin al’umma a yankin Kourfeye Filingue a cikin jihar Tillabery sun bukaci mahukuntan kasar da su dauki matakan gaggawa domin karshen kashe-kashe da ke faruwa a yankin.


A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata an samu asarar rayukan jama’a da dama sakamakon irin wadannan hare-hare.

Yayin da ayke yiwa Sashin Hausa ba RFI akan matsalar, Alhaji Ibrahim Barke Doka, daya daga cikin shugabannin al’umma a yankin na Kourfeye, ya zargi jami’an tsaro da nuna sakaci.

Barke ya kara da cewa a halin da ake ciki, jama’ar yankin da wannan matsala ta shafa suna cikin firgici, wanda ka iya hana manoma damar gudanar da ayyukansu, abinda ya bayyana a matsayin babbar barazana.

Al'ummar Filingue sun koka bisa hare-haren 'yan bindiga 07/05/2018 - Daga Abdoulkarim Ibrahim Saurare