rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyoyin fararen hula a Nijar sun nemi Macron ya sa baki a saki mambobinsu

media
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da na Nijar Mahammadou Issoufou wani lokaci a 2017 LUDOVIC MARIN / AFP

Kungiyoyin fararen hula a jamhuriyar Nijar sun bukaci shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron daya sa baki, shugaban kasar Nijar Issoufou Mahammadou ya saki mambobinsu da gwamnatinsa ke ci gaba da rikewa, sakamakon fafutukar da suke ta neman sauyi a tafiyar harkokin gwamnatin.


A daidai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke shirin ganawa da takwarana na Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou yau litinin a birnin Paris, kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasashen duniya da dama ne ke yin kira ga shugaba Macron da ya urmuci Issifou Mahamadou domin ya saki magoya bayan kungiyoyin fararen hula da aka cafke yau sama da watanni biyu a sassan kasar.

Laurent Duarte, shugaban kungiyar Tournons la page au Secours catholique, na daya daga cikin wadanda suka yi wannan kira Macron '

Muna kira ga Emmanuel Macron da ya yi amfani da wannan damar domin jan hankalin shugaban Nijar kan mutunta ka’idojojin dimokradiyya da kuma kare hakkin bil’adama.

Babban abin da muke bukata shi ne Faransa ta tsaya tsayin daka domin tabbatar da cewa an saki magoya bayan kungiyoyin fararen hula da ke tsare a kasar, domin samun zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali a kasar ta Nijar.

Ya kamata Faransa ta sani cewa, babban makamin da ya kamata a yi amfani da shi domin yaki da ayyukan ta’addanci a wannan zamani shi ne tabbatar da adalci da kuma mutunta ‘yancin dan adam.

Bai kamata a ce Faransa na ikirarin cewa tana yaki da ta’addanci a kasashen Nijar, Mali ko kuma Chadi ba a daidai lokacin da gwamnatocin wadannan kasashe ke tauye wa jama’a hakkokinsu ba'.