rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Muhammadou Issoufou na Nijar ya ce kama 'yan kungiya bai saba wa Doka ba

media
Muhammadou Issoufou na Nijar ya ce kama 'yan kungiya bai saba wa Doka ba REUTERS/Philippe Wojazer

Shugaban jamhuriyar Nijar Issifou Mahamadou wanda a jiya litinin ya gana da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a birnin Paris, ya ce ba inda gwamnatinsa ta saba wa doka sakamakon kama shugabannin kungiyoyin fararen hular kasar 26 saboda yin zanga-zangar adawa da dokar kasafin kudin kasar ta bana.


Issifou Mahamadou ya bayyana wa manema labarai cewa Niger kasa da ke bi tare da mutunta tsarin dimokradiyya.

Ya ce ina jin cewa masu fadar haka ba su san kasar Nijar da kuma abubuwan da ke faruwa a can ba. Nijar kasa ce ta dimokuradiyya da ke kare hakkokin bil’adama.

Abin da ya faru shi ne, wasu kungiyoyi sun bukaci shirya zanga-zanga a tsakiyar dare, dauki misalin cewa wasu za su yunkurin shirya zanga-zanga tsakiya dare a nan birnin Paris, anya mahukunta za su amince da haka? Nijar, kasa ce da ke da dokoki irin wadannan ake amfani da su a biranen Paris, ko Washington, ko Rome, ko London ko kuma Berlin.

Ina son ku fahinci cewa a Nijar kungiyoyin fararen hula sun kasu gida biyu, akwai wadanda ke aikin gina dimokuradiyya da kuma wadanda ke ko kokarin hambarar da gwamnati, wadannan mutane ne da suka saba yakar duk wata gwamnatin dimokuradiyya.

Saboda haka ni ba zan bayar da umurnin cewa a sake su ba, domin kundin tsarin mulki ya fayyace matsayin bangaren zartaswa da na shari’a, alkalai ne kawai ke da hurumin daukar irin wannan mataki.