rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Ghana

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Al'ummar Jamhuriyar Nijar na bukukuwan karamar Sallah

media
Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou tare da sauran manyan mukarrabansa yayin Sallah a babban masallacin birnin Niamey. iinanews.org

Yau Alhamis al’ummar Musulmi a Jamhuriyar Nijar na gudanar da shagulgulan bikin karamar Sallah bayan ganin jinjirin watan Shawwal a sassa da dama na kasar a yanmacin jiya Laraba.


Majalisar koli ta harkokin addinin Islama ta kasar ce ta tabbatar da ganin watan a garuruwa da dama na jihohin Diffa da kuma Damagaram-Zinder, bayan share tsawon kwanaki 29 ana gudanar da azumin watan Ramadana.

A kasar Ghana kuwa majalisar kolin addinin musuluncin kasar ta umurci jama’a da su ajiye azumin a yau, bayan da aka ga jinjirin watan Shawwal a yankin Kumasi, sai dai ya ce ba za a yi sallar idi ba sai gobe Juma’a.

A game da Sallar da ake yi a Nijar, wakilinmu Salisu Isa ya aiko mana rahoto daga Maradi.

Al'ummar Jamhuriyar Nijar na bukukuwan karamar Sallah 14/06/2018 - Daga Salisu Isah Saurare