Boko Haram ta kashe dakarun Nijar 10
Rahotanni daga jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar dakarun kasar 10 yayin da wasu 4 suka bata, sakamakon wani harin kwonton-bauna da mayakan Boko Haram suka kai masu a cikin daren Asabar zuwa wayewar garin jiya lahadi.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar tsaron kasar ta ce, lamarin ya faru ne a wani wuri da ke cikin jihar Diffa kusa da yankin tafkin Chadi, kuma kafin su arce, maharan sun kona motocin soji akalla uku.
A cikin watan Afrilun da ya gabata ne, gwamnatin Nijar ta sanar da kaddamar da wani aikin soji da zimmar kakkabe mayakan Boko Haram a yankin tafkin Chadi da ya hada kasashen Nijar da Chadi da Najeriya da kuma Kamaru.
A bangare guda, a yau Litinin ake fara shara’ar mutanen da ake zargin cewa mayakan Boko Haram ne a garin na Diffa, karo na farko, duk da cewa kawo yanzu ba a san adadin wadanda za su gurfana a gaban kotun ta musamman ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu