rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Hakkin Mata Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mataimakiyar sakataren MDD na ziyara a Nijar

media
Amina Muhammad, mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniya yayin da ta isa Jamhuriyar Nijar RFIHAUSA

Amina Muhammad, mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya na ziyara a Jamhuriyar Nijar, inda a yau ta ziyarci Jihar Maradi don gani da ido, kan irin ayyukan da hukumomin Majalisar ke yi keyi kan hakkokin yara, ilimin mata, kiwon lafiya, da kananan sana’o’in mata sannan da batun canjin yanayi.


A ranar Asabar 7 ga watan Yuly na shekarar 2018, mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniyar ta soma ziyarar a Jamhuriyar Nijar.

A cewar Amina Muhammad babban makasudin ziyarar shi ne karfafa samar da hakkokin mata a fannonin Ilimi, Lafiya da kuma basu damar shiga al’amuran siyasa wajen tafiyar da al’amuran mulkin kasa.

Wakilinmu daga Maradi Salisu Isa ya aiko mana da Rahoto.

Mataimakiyar sakataren MDD na ziyara a Nijar 08/07/2018 - Daga Salisu Isah Saurare