Isa ga babban shafi
Nijar

Kotu ta daure 'yan Boko Haram a Nijar

Wata kotu da ke yi wa 'ya'yan kungiyar Boko Haram shari’a a Jamhuriyar Nijar ta yanke wa mutane 17 hukuncin daurin shekaru daban-daban saboda da samun su da hannu cikin ayyukan ta'addanci na kungiyar.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram pmnewsnigeria
Talla

Mai gabatar da kara, Chaibou Samna, ya ce daga cikin mutane 42 da aka gabatar a gaban kotun, 17 sun samu daurin tsakanin shekaru 2 zuwa 7, yayin da aka salami 21 saboda rashin samun shaida a kansu.

Daya daga cikin jagororin Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta CIDDH a Maradi,   Muhammadu Buhari ya yaba da wannan mataki na kotu, in da ya ce, dama ya dace a hukunta masu laifi don zama izina ga al'umma.

Sai dai ya bukaci gwamnatin Nijar da ta yi nazari kan musabbabin shigar matasan cikin Boko Haram don gano bakin zaren magance matsalar ta'addanci cikin sauki, yayin da ya ce, talauci na daya daga cikin abubuwan da ke jefa matasan cikin wannan hali, abin da ke bai wa Boko Haram damar yaudarar su da kudade.

"Gwamnati ya kamata ta kirkiro wani tsari na bai wa matasa aikin yi" in ji Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.