Isa ga babban shafi
Nijar-Aljeria

kimanin Bakin Haure 439 aka ceto a hamadar arewacin Nijar

Hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da ceto mutane 439 a cikin yankin Hamadar arewacin kasar Nijar kusa da iyakar kasar da Algeria.Hukumar ta OIM ta ce mutanen sun fito ne daga kasashe 13 na Yammacin Afirka, da suka hada da mata da kananan yara.

Logótipo da OIM - Organização Internacional das Migrações
Logótipo da OIM - Organização Internacional das Migrações OIM/IOM
Talla

Ko a ranar 4 ga wannan wata na Seftamba ma wasu bakin haure yan afrika su 92 sun isa a wannan yankin kafin a ceto su.

Hukumar dake kula da kaurar bakin ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, mahukumtan birnin Alje na kasar Aljeriya ne, suka koro bakin hauren, kamar kamar yadda ya faru bada dadewa ba, inda suka koro dubban bakin haure suka kuma watsar da su a rairaiyi hamadar kasar ta Jamhuriyar Nijar

Hukumar ta 'OIM ta ce an sauke mutane ne a sansanin wucin gadi dake garin Arlit a arewacin jamhuriyar Nijar, inda take fatan ganin ta isar da su a kasashensu na Asali

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.