rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Bakin-haure Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

IOM ta ceto bakin-haure sama da 70 daga hamada

media
Wasu bakin-haure uku yayin da suka tunkari arewa son isa Algeria, bayan ketare kan iyakar garin Assamaka dake arewacin Jamhuriyar Nijar a ranar Lahadi, 3 ga Yuni, 2018. Jerome Delay / ASSOCIATED PRESS

Hukumar kula da bakin-haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce jami’anta sun ceto mutane 74 daga cikin yankin hamadar da ke arewacin Jamhuriyar Nijar kusa da iyakar kasar da Algeria.


Hukumar ta OIM ta ce akwai mace daya da kuma kananan yara biyu a cikin wadanda aka ceton bayan sun share tsawon kwanaki suna tafiyar kafa a kusa da garin Assamaka.

‘Yan gudun hijirar da aka ceto sun fito ne daga kasashen yammacin Afirka 9, wato Najeriya, Burkina Faso, Côte d'Ivoire, Mali, Gambie, Niger, Guinée Conakry, Guinée Bissau da kuma Liberia.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta MDD ta ce ko a farkon watan Satumban da ya gabata, jami’anta sun ceto wasu bakin-hauren 439 da suka fito daga kasashen yammacin Afrika a yankin Hamadar na arewacin jamhuriyar Nijar.