Isa ga babban shafi
Nijar

Mata 3 daga cikin 15 da ‘yan Boko Haram suka sace a Diffa sun tsere

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa uku daga cikin mata 15 da ‘yan Boko Haram suka sace a ranar 24 ga watan Nuwamba a yankin Diffa da ke daf da kan iyaka da Najeriya sun tsere, inda yanzu haka suke hannun mahukuntan kasar.

Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar, yayin aikin sintiri a yankin Diffa, dake iyaka da Najeriya. 21/6/2016.
Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar, yayin aikin sintiri a yankin Diffa, dake iyaka da Najeriya. 21/6/2016. REUTERS/Luc Gnago.
Talla

Wata kungiya mai suna Urgence Diffa ta tabbatar da cewa wani lokaci a yau ne mahukunta a yankin na Diffa za su mika matan uku da suka kubuta a hannun iyalansu.

A cikin daren ranar 24 ga watan Nuwamba ne ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari tare da sace ‘yan mata 9 a garin Blaharde da kuma wasu 6 a garin Bandé da ke kusa da Toumour.

Zalika rahotanni sun kuma tabbatar da cewa kafin sace ‘yan matan 9, akwai wasu mata da kananan yara fiye da 30 da kungiyar ta Boko Haram ta sace a garin Ngalewa a jihar ta Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.