Isa ga babban shafi
Nijar

"Mayaka sun tilastawa mutane dubu 52 barin muhallansu a Nijar"

Majalisar dinkin duniya, ta ce hare-haren mayaka masu da’awar jihadi ya tilasatawa sama da mutane dubu 52,000 tserewa muhallansu a yammacin Jamhuriyar Nijar, daga watan Janairun shekarar 2018 zuwa yanzu.

Wasu 'yan gudun hijira da hare-haren Boko Haram ya raba da muhallansu.
Wasu 'yan gudun hijira da hare-haren Boko Haram ya raba da muhallansu. AFP Photo/ISSOUF SANOGO
Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar majalisar ta ce, hare-haren na baya bayan nan, sun shafi wasu yankunan Tahoua da Tillaberi, dake kan iyakar jamhuriyar ta Nijar da kasashen Mali da Burkina Faso, inda gwamnati ta tsawaita dokar ta bacin da ta kafa.

Rahoton majalisar ya ce’yan gudun hijirar da suka tsere sun bayyana cewa maharan sun matsa ainun wajen kaiwa kauyuka hare-hare, kisa da satar mutane, kone makarantu da kuma satar dukiya.

Rahoton ya kara da cewa jami’an agaji basa iya kaiwa zuwa yankunan da tashin hankalin yafi shafa, saboda barazanar fuskantar hare-haren mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.