rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Mahamadou Issoufou

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Nijar ta daure hafsoshin soji shekaru 15

media
An samu sojojin da laifin yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Issofou Muhammadou REUTERS/Francois Rihouay

Kotun daukaka kara a Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 5 zuwa 15 da ta yanke wa wasu manyan hafasoshin sojin kasar su 8 da kuma wani farar hula daya, bayan samun su da laifin yunkurin kifar da gwamnati a shekara ta 2015.


Manyan hafsoshin soji uku ne aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari, da suka hada da Janar Salou Souleyman, tsohon babban kwamandan askarawan kasar da Laftanar Ousman Hambaly wanda tun a shekara ta 2010 aka cafke shi tare da gurfanar da shi a gaban wata kotun soji saboda irin wannan zargi na yunkurin juyin mulki, kafin a wanke shi a shekara ta 2012 daga wannan zargi.

Yayin da aka yanke wa wadannan sojoji hukuncin daurin shekaru 15, akwai wasu sojoji uku da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru uku-uku, yayin da wasu sojoji biyu da farar hula daya cikinsu har da Niandou Salou, dan janar Salou Souleyman da aka yankewa hukuncin daurin shekaru biyar-biyar.

A wancan lokaci dai masu shigar da kara, sun bayyana wa kotu cewa, mutanen sun tsara yadda za su cafke shugaban kasar Issifou Mahamadou da kuma babban kwamandan askarawan da ke kare shugaban a ranar 18 ga watan Disamba, lokacin da yake dawowa daga birnin Maradi da ke tsakiyar kasar bayan kammala bukukuwan zagayowar ranar Jamhuriya a shekara ta 2015.

Tabbatar da wannan hukunci da kotun ta yi a ranar Laraba, na zuwa ne a dai dai lokacin da rahotanni ke cewa yanzu haka, ana ci gaba da tsare wasu manyan jamiā€™an soji da kuma fararen hula da ake zargi da shirya wani juyin mulki a kasar.