Nijar ta janye dokar haramta sana'o'i a Diffa
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta cire dokar da ke hana kamun kifi, noman tattasai da sauran amfanin gona a zagayen kogin Komadugu a jihar Diffa, dokar da aka kafa bisa zargin cewa ‘yan Boko Haram na amfani da wadannan sana’o’i don samun kudade tsawon shekaru hudu da suka gabata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wata majiya a ma’aaikatar cikin gidan kasar ta Nijar, ta ce an cire dokar ne lura da yadda ake kara samun zaman lafiya a yankin da ke gaf da iyakar Nijar da Najeriya.
Wata kungiyar agaji mai zaman kanta OXFAM, ta ce a kowace shekara manoman yankin na samun sama da Euro milyan 42 sakamakon noman tattasai da kuma kamun kifin a yankin.
Sai dai tattalin arzikin yankin ya gamu da gagarumar matsala saboda dokar haramcin sana’o’in, lamarin da ya jefa dubban jama’a cikin talauci a yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu