Isa ga babban shafi
Nijar

Majalisar Dokokin Nijar ta amince da sabuwar dokar zabe

Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar ta amincewa da sabuwar dokar zabe, to sai dai ‘yan adawa sun fice daga zauren Majalisar lokacin da aka fara tafka mahawara dangane da wannan doka.

Majalisar dokokin jamhuriyar Nijar, dake birnin Niamey.
Majalisar dokokin jamhuriyar Nijar, dake birnin Niamey. AFP/Sia Kambou
Talla

‘Yan majalisa 133 ne suka amince da wannan doka, wanda ministan cikin gidan kasar Bazoum Mohamed ya gabatar amadadin gwamnati, yana mai cewa dokar ita ce mafi kyau da za ta bayar da damar shirya kyakkyawan zabe a kasar ta Nijar.

Bazoum Mohamed wanda ke shirin tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2021, ya ce lura da halin na rashin tsaro da kasar ke fama shi, gwamnati ba za ta yi kuskuren zuwa zabe a cikin yanayi na rashin jituwa ba a cikin kasar, saboda haka ne aka samar da sabuwar dokar.

To sai dai tun kafin fara mahawara dangane da daftarin dokar ne ‘yan adawa suka fice daga zauren majalisar domin nuna rashin amincewa da sabuwar dokar.

To sai dai kafin su fice daga zauren, ‘yan adawar sun gabatar da kudurin da ke neman kada kuri’ar yankan kauna don tsige Firaministan kasar Briji Rafini, duk da cewa abu ne mai wuya bukatar ta samu karbuwa, lura da cewa gwamnati na da cikakken rinjya a cikin majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.