rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Ta'addanci BOKO HARAM ISIL

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

IS ta dauki alhakin halaka sojin Nijar 18 a sansaninsu

media
Wasu dakarun Jamhuriyar Nijar. 19/2/2019. US Army/Richard Bumgardner

Tsagin mayakan Boko Haram da ya yiwa kungiyar IS mubaya’a da aka fi sani da ISWAP, ya dauki alhakin harin da aka kai kan wani sansanin sojin Nijar a ranar litinin da ta gabata.


Akalla sojojin Jamhuriyar Nijar 18 mayakan na Boko Haram suka halaka a farmakin kan sansanin sojin kasar da ke kan iyakarta da Mali.

Da fari wasu yan kunar bakin wake biyu ne suka tarwatsa kansu a kofar shiga sansanin na INATES da ke gaf da iyakar Nijar da Mali, daga bisani kuma wasu mayakan suk afkawa dakarun sojin da barin wuta.

Bayan shafe awanni ana musayar wuta da kuma jikkata dakarun na Nijar ne, sojojin suka samu rinjaye kan mayakan na Boko Haram da taimakon jiragen yakin Amurka da Faransa, da kuma Karin wasu sojin na Nijar daga kasa.

Nijar na cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da matsalolin tsaro na mayaka masu da’awar jihadi, ciki har da na Boko Haram.

A shekarar 2016, ISWAP ya balle da cikin kungiyar Boko Haram da Abubakar Shekau ke jagoranta.