rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jamhuriyar Nijer zata samar da fagen kasuwanci da bunkasa masana'antu

media
Shugaban jamhuriyar Nijer, Issoufou Mahamadou ONEP-NIGER

A karo na farko jamhuriyar Nijer zata na samar da fagen kasuwanci da bunkasa masanaantu da kuma fitar da haja a kasashen ketare

A cewar majiyar an dauki wannan mataki na samar dawannan fage na bunkasa tattalin arzikin kasar ta mahuriya nijer ne, a lokacin taron majalisar ministocin na ranar 26 g watan yulin da ya gabata za a kuma gina cibiyar hukumar ne a birnin Niamey.


Shafin yanar gizon fadar shugabancin kasar ta Nijer ya ce, babbar manufar da shirin ke son cimmawa ita ce, samar da fagen bunkasa tattalin arzikin, masana’antu da zai zaburar da fitar da hajojin da su ke samarwa zuwa ketare,

A cewar sanarwar Tun bayan samun yancin kan kasar ta jamhuriyar Nijer a 1960, an yi amfani da dubaru da dama wajen bunkasa masana’antu a kasar, hakan bai bada damar ciyar da masana’antu da kamfanonin kasar gaba, kamar yadda ake bukata ba.

Wata takardar ofishin ministan masana’antu da AFP takai gareta ta ce, Masana’antu kasar ta Nijer na samar da kashi 4% ne kacal daga cikin kudaden shigar da kasar ke samu a shekara

Duniya nayiwa kasar ta jamhuriyar Nijer dake yankin Sahel daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, duk kuwa da kasancewarta maiarizikin ma’adanin Uranium da man fetur. Ga kuma zinare awani gefen,

Tana kuma samun mafi yawan kudaden shigarta ne ta fannin ma’adanan karkashin kasa, Noma da kuma kiyo.