rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Nijar Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dubban 'yan Nijar sun yi zanga-zanga a birnin Yamai

media
'Yan Nijar 2000 sun shiga zanga-zangar adawa da gwamnati. Nigerdiaspora

Kimanin mutane dubu 2 ne suka gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Yamai, bisa bukatar neman gudanar da sauye-sauye ga tsarin zaben kasar, da kuma nuna adawa ga gwamnati, saboda gazawar da suke zarginta da yi.


Zanga-zangar ta zo ne wata guda bayan hukumar zaben kasar, ta fitar da jawadalin zaben shugaban kasa, da na ‘yan majalisu da za a yi a ranar 27 ga Disamban 2020 sai kuma na kananan hukumomi da kuma yankuna, da za su gudana a watan Nuwamban shekarar.

Masu zanga-zangar ciki har da magoya bayan tsohon fira Minista Hama Amadou, sun bukaci cikakkun bayanai daga gwamnati, kan kudaden da take warewa bangaren tsaro, gami da sauran bukatu da ma.

Masu zanga-zangar da suka taru a gaban zauren majalisar kasar ta Nijar sun sha alwashin ba za su kwance damarar da suka daura ba, har sai burinsu ya cika.

Cikin watan Yuni Majalisar Dokokin Nijar ta amincewa da sabuwar dokar zabe, to sai dai ‘yan adawa sun fice daga zauren Majalisar lokacin da aka fara tafka mahawara dangane da dokar.

‘Yan majalisa 133 ne suka amince da dokar, wanda ministan cikin gidan kasar Bazoum Mohamed ya gabatar a madadin gwamnati, yana mai cewa dokar ita ce mafi kyau da za ta bayar da damar shirya kyakkyawan zabe a kasar ta Nijar.