rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Salah zai buga wasan da Masar za ta fafata da Rasha

Hukumar kwallon kafa ta Masar, ta ce dan wasan kasar Muhd Salah, ya samu isasshiyar lafiyar, buga wasan da Masar din za fafata ranar Talata, tsakaninta da Rasha. Salah dai bai samu buga wasan farko da Masar ta yi rashin nasara a hannun Uruguay da 0-1 kwallo daya mai ban haushi ba, a ranar Juma'a, a dalilin rauni da ya samu a kafadarsa yayin wasan karshe na 26 ga watan Mayu, da kungiyarsa da fafata da Real Madrid.