Mu Zagaya Duniya
Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Matakin Najeriya na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar
Daga cikin labarun da shirin ya kunsa a wannan makon, akwai matakin da Najeriya ta dauka na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar, tare da janye baki dayan takunkuman da ta kakaba mata.Gwamnatin Birtaniya ta ce a shirye take ta baiwa ‘yan dubban ‘yan Rwanda da ke neman mafaka fam dubu uku kowannensu, to amma fa a bisa sharadin za su amince a mayar da su gida daga kasar ta Birtaniya16/03/202419:19 -
Wasu daga cikin muhimman labarun da suka wakana a makon da ya gabata
Za a ji yadda aka sake zabar sabuwar ranar gudanar da zaben shugabancin kasar Senegal,Al’ummar Sudan ta Kudu sun tsallake rijiya da baya, domin kuwa aniyar wani sabon mugu da ya bayyana ce ta watse bayanda ya yi kokarin shirya juyin mulki a kasar, duk da cewar har yanzu basu gama murmurewa daga kazamin yakin basasar da ya tagayyara su ba, wato dai ana kukan targade karaya kuma na neman kunno kai.09/03/202420:02 -
Wasu daga cikin muhiman labaren mako daga Rfi- Rikicin jihar Kano
Al’ummar Jihar Kano dake Najeriya sun tashi da labarin murabus din da shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukamin sa, sakamakon abinda ya kira sanyaya masa gwuiwar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, wajen sukar yadda suke gudanar da aikin su.Wannan murabus din ta haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen jihar Kano, tare da hudubobi a Masallatan Juma’a dangane da muhimmancin hukumar da kuma rawar da take takawa.Nasirudeen Muhammed zai jagoranci shirin.02/03/202420:21 -
Jana'izar ma'aikacin RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou a garin Tsibirin Gobir
A jiya Juma'a 17 ga watan Fabrairun 2024 ne aka gudanar da jana'izar ma'aikacin RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou a garin Tsibirin Gobir, Mahammane Salissou Hamissou wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Larabar da ta gabata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.17/02/202420:10 -
Matakin hadin gwiwar da Nijar ,Mali da Burkina Faso suka dauka, na sanar da ficewa daga ECOWAS
Daga cikin muhimman labarun makon jiya da shirin ya sake waiwaya domin bitarsu akwai, matakin hadin gwiwar da Nijar da Mali da kuma Burkina Faso suka dauka, na sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS.Sai kuma sake karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi, karo na biyu cikin watanni 8.A Turai kuwa, za a ji yadda zanga-zangar manoma ta bazu zuwa sassan nahiyar saboda adawa da wasu sauye-sauyen mahukuntan kasashen yankin da suka ce ba za su lamunta ba.03/02/202419:58 -
Taron Shugabannin arewacin Najeriya don lalubo hanyar magance matsalar tsaron
Masu sauraro Assalamu alaikum, Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI ke muku maraba cikin shirin Mu Zagaya Duniya da ke waiwaye gami da zabar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.27/01/202419:56 -
Rikici tsakanin 'yan ta'adda a arewacin Najeriya ya illata bangaren Dogo Gide
Shirin wannan makon zai fara ne da waiwayar bata-kashin da aka yi tsakanin ‘yan bindiga a Najeriya, lamarin da ya kai ga illata bangaren daya daga cikin jagoran ‘yan ta’adddan da ya addabi jama’a.Fira Ministan Jamhuriyar Nijar ya yi tatttaki zuwa Iran, bayan ganawarsa da mahukuntan kasar Rasha inda suka karfafa yarjejeniyar tsaron da suka kullla.20/01/202419:49 -
Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Abba Gida-Gida a zaben gwamnan Kano
Cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman, ya fara ne daga Kano a Najeriya, inda a ranar Juma’ar da ta gabata, kotun koli ta tabbatar da gwamna Abba Kabir Yusuf Abba na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen gwamnan jihar.15/01/202420:01 -
Gwamnatin Najeriya ta haramta karbar shaidar karatun digiri daga Benin da Togo
Daga cikin labarun da shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya sake waiwaya a wannan makon akwai matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na haramta karbar takardun shaidar kammala karatun digiri daga jami'o'in Jamhuriyar Benin da kuma kasar Togo.15/01/202419:45 -
Bitar wasu muhimman labaran da suka faru a duniya cikin wannan mako
Daga cikin labarun da Shirin ya kunsa akwai batun yadda yan ta'adda a Najeriya ke gina ramu suna boyewa, saboda barin wutar da suke sha daga sojojin kasar, sai kuma batun kammala ficewar sojojin Faransa a Nijer da dai sauran manyan labaran da suka hada da Burkina Faso, jamhuriyar Benin, yakin Isra'ila da Hamas, tare da dokar yan ci rani da Faransa ta amince da ita.23/12/202320:04 -
ECOWAS/CEDEAO ta tabbatar da juyin mulki aka yi a Nijar
Daga cikin labarun da Shirin ya kunsa akwai matakin da kungiyar kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ko CEDAEO ta dauka na amincewa da da cewar an yi juyin Mulki a Nijar, sannan kuma ta dakatar da ita daga cikin ta har sai lokacin da sojoji suka maida wa farar hula Mulki.A Najeriya kuma, Bankin Duniya ne ya bukaci gwamnatin kasar ta fadada tsauraran matakan da take dauka na yi wa tattalin arzikin kasar garambawul, domin ceto shi daga durkushewa baki daya a nan gaba.16/12/202320:31 -
COP28 - An samar da asusun tallafa wa kasashe don yaki da matsalar sauyin yanayi
Shirin "Mu zagaya duniya" na wannan makon tare da Khamis Saleh ya waiwari babban taron sauyin yanayi na COP28 da aka faro a Dubai, inda aka samar da wani asusu na musamman da manyan kasashe za su rinka zuba kudi don taimaka kananan kasashen da matsalar da ba su suka samar ba ta fi shafa.02/12/202319:46 -
Bitar wasu daga cikin labaran da suka dauki hankali na mako
Shirin zai kuma waiwayi kalaman da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayi kan cewa Dimokaradiyar kasashen yammacin turai fa ba ta haifa wa nahiyar Afirka da mai idanu ba.25/11/202319:50 -
MU zagaya Duniya: Kotun daukaka kara a Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Kano
Ciki Shirin wannan makon za a ji cewar Kotun Daukaka karar Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben Kano da ya karbe kujerar Gwamnan jihar daga hannunn Abba Kabir Yusuf na NNPP ya mika ta zuwa Nasir Yusuf Gawuna na APC.Kasar Ghana ta bukaci hadin gwiwar kasashen Afirka domin tilasta wa kasashen da suka yi wa nahiyar mulkin mallaka biyansu diyya akan yadda suka azabtar da su da cinikin bayi.18/11/202319:55 -
wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a wannan makon
Halin da asibitoci ke ciki a Zirin Gaza, bayan da aka shafe sama da wata guda Isra’ila na ci gaba da ruwan bama-bamai kan Falasdinawa, wadanda ya zuwa yanzu akalla dubu 40 suka jikkata baya ga sama da 10 da suka mutu a Gaza tareda Nura Ado Suleiman.11/11/202319:58
Mu Zagaya Duniya
Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.