Wasanni
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Masar ce ta daya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Afrika da aka yi a Ghana
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako yayi duba ne kan yadda gasar guje-guje da tsalle -tsalle ta nahiyar Afrika ta gudana a kasar Ghana. Kasar Masar ce ta zamo zakarar lashe lambobin yabo har 189, sai Najeriya da ke bi mata da lambobn yabo 120, yayinda Janhuriyar Nijar ta lashe lambobin yabo 11, lamarin da ya bata damar zama amatsayi na 16 a teburin kasashe 53 da suka halarci gasar bayan da Cape Verde ta janye daga fafatawa a wannan karon.25/03/202409:58 -
Sharhi kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai za su gudana
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai za su gudana. A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai hukumar kula da wasan kwallon kafar Turai UEFA ta hada yadda kungiyoyi 8 da suka yi saura a gasar zakarun Turai z asu kara da junanansu. Tsohon kyaftin din Najeriya wanda kuma ya taba lashe gasar da kungiyar Chelsea Mikel John Obi ne ya jagoranci hada yadda kungiyoyin za su kara da juna.18/03/202409:59 -
Ci gaban da aka samu a wasan damben gargajiya a Najeriya
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne kan irin ci gaban da aka samu a bangaren wasan damben gargajiya a Najeriya.11/03/202409:59 -
Yadda aka kammala zangon farko na gasar kwallon kafa ta Firimiyar Najeriya
Shirin awanan lokaci zai nazari game da yadda zangon farko na gasar Firimiyar Najeriya ya kammala, inda tuni aka juya zagaye na biyu na gasar ta kwararru.Shirin ya kuma duba batun soma gasar a kan lokaci da kuma batun daukar nauyi, sai kuma batun rashin ingancin filaye, baya ga kuma karanchin samun bayanan ‘yan wasan da ke taka leda a gasar.Latsa alamar sauti don sauraron shirin:04/03/202410:00 -
Nazari kan komawar Kylian Mbappe kungiyar Real Madrid a kaka mai zuwa
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi nazari ne kan komawar dan wasan gaba na kungiyar PSG, Kylian Mbappe kungiyar Real Madrid a karshen kakar bana. Yanzu dai za a iya cewa an yi ta, ta kare bayan da a ranar 13 ga wannan watan ne dan wasan mai shekara 25 ya sanar da kungiyarsa PSG batun sauya shekarar tasa da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kakar watan Yuni.26/02/202409:59 -
Yadda aka gudanar da gasar Polo ta bana a garin Jos
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya mai da hankali ne kan yadda aka gudanar da gasar Polo a Jahar Filato da ke arewacin Najeriya. A wannan karo, club club din wasan kwallon dawakin da suka fafata a gasar sun fito ne daga jihohin Lagos, Nasarawa, Bauchi, Taraba, Kaduna, Kano, Niger da kuma Katsina. A karshe dai club din Keffi Ponies ta jihar Nasarawa ta lashe gasar a karawar karshe da suka yi da Malconmines daga Filato mai masaukin baki.19/02/202409:55 -
Yadda Ivory Coast ta lashe kofin AFCON bayan ta doke Najeriya
A daren jiya Lahadi ne aka kammala gasar lashe kofin Afrika AFCON karo na 34 da Ivory Coast ta karbi baukunci kuma daga bisa ta lashe gasar. Najeriya ce ta fara zura kwallon farko ta hannun William Ekong tun kafin a tafi hutun rabin lokacin, sai dai bayan dawowa ne tawagar ta Elephants ta farke ta hannun Kesse kafin daga bisani a minti na 81 ta kara kwallo ta hannun Sebestin Hallar wacce ta bata nasara.12/02/202409:58 -
Mai masaukin baki Ivory Coast ta lashe kofin AFCON bayan doke Najeriya
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh, ya mayar da hankali ne kan yadda ta kaya a wasan karshe na cin kofin AFCON wanda Ivory Coast mai masaukin baki ta lashe bayan doke Najeriya da kwallaye 2 da 1.12/02/202409:58 -
Yadda wasannin zagayen Kwata final suka kaya a gasar AFCON
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan lokacin yayi nazari ne akan wasannin matakin dab da na kusa da na karshe wato na zagayen Kwata final da aka yi a gasar AFCON.05/02/202410:00 -
Matakin zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar lashe kofin Afrika AFCON
A yau Juma’a nan ce dai za a fara buga wasannin zagen dab da na kusa da na karshe a gasar lashe kofin Afrika AFCON da ke gudana a kasar Ivory Coast.Za kuma a fara karawar ne tsakanin Najeriya da Angola karfe shida agogon Najeriya, kafin da misalign karfe 9 a buga wasa tsakanin DR Congo da Guinea.A wasannin gobe Asabar, akwai karawa tsakanin Mali da Cote d’Ivoire sai kuma Cape Verde da Afrika ta Kudu.02/02/202409:59 -
Nazari kan karawar da aka yi tsakanin Najeriya da Kamaru a gasar AFCON 2023
A ranar asabar ne dai aka fafata tsakanin tawagar Super Eagels ta Najeriya ta tawkararta ta Indomitable Lions ta Kamaru, a wasan zagayen ‘yan 16 a gasar lashe kofin Afrika AFCON da Ivory Coast ke karbar bakunci.Wannan wasa dai ya ja hankali a wannan gasa, ganin yadda kasashen biyu ke da suna a fagen kwallon kafar Afrika, sannan kuma akwai dadaddiyar hamayya a tsakaninsu.29/01/202410:00 -
Najeria da Kamaru za su fafata a zagaye na 2 na gasar AFCON
Najeriya karkashin mai horar da kungiyar Jose Peseiro za ta nemi kare maratabar ta da kuma neman ganin ta tsallaka mataki na gaba a wanan gangami,yayida a daya wajen ,Kamaru a cewar mai horar da ita ,Rigobert Song za su kasance a kan bakar su na ganin su doke Najeriya.26/01/202409:57 -
Yadda kasashe ke bayar da mamaki a wasannin gasar AFCON a Ivory Coast
Shirin duniyar wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali kan yadda gasar AFCON ke ci gaba da gudana a Ivory Coast, gasar da zuwa yanzu aka kammala zagaye biyu na matakin rukuni.22/01/202409:57 -
Yadda aka kammala wasannin farko na rukuni a gasar AFCON
Shirin "Duniyar Wasanni" a wannan lokaci zayyi duba ne akan yadda aka kammala wasannin farko na matakin rukuni da kuma yadda aka faro na biyu a gasar AFCON da ke gudana a Ivory Coast. An kuma fara wasannin ne da karawar da aka yi tsakanin Equatorial Guinea Guinea-Bissau, inda Equatorial Guinea ta samu nasara akan Guinea-Bissau da ci 4-2.19/01/202409:59 -
Gasar cin kofin kasashen Afirka ta kankama a Ivory Coast
A ranar asabar da ta gabata ne aka fara gasar lashe kofin nahiyar Afrika wato AFCON da kasar Ivory Coast ke karbar bakunci.15/01/202409:59
Wasanni
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.