rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Chadi ya kafa dokar ta baci a gabashin kasar

Shugaban Chadi Idris Deby ya kafa dokar ta baci a wasu yankuna biyu dake gabashin kasar, bayan fuskantar tashin hankalin fadan kabilanci, da yayi sanadin mutuwar mutane 50, cikin wannan wata na Agusta. Dokar ta bacin da shugaban na Chadi ya kafa za ta shafe tsawon watanni uku tana aiki, a karkashin sa idon dakarun sojin kasar.