Isa ga babban shafi
Najeriya

Kingibe ba zai yi takara da Buhari ba

Najeriya : Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Babagana Kingibe, ba zaiyi takara da shugaban kasar Muhammadu Buhari ba a zaben shekara ta 2019.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja RFIHausa/Kabiru Yusuf
Talla

An dai ga hutunan kamfe din Kingibe mammanne a Abuja babban birnin kasar, da ma wasu biranen Najeriya.

A shekarar 1991 tsohon jami’in diflomasiyyar ya yi takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar (SDP) inda ya fadi a matakin fitar da yan takara.

Yayin da ya nemi mataimakin shugaban kasa tare da Moshood Abiola a zaben shekarar 1993, zaben da shugaban mulkin soji na wancan lokacin, Ibrahim Babangida ya rusa.

Bazuwar hotunansa a wasu manyan biranen kasar ya haifar da rade-radin cewar yana da muradin yin takara a shekara ta 2019.

A cikin sanarwa da ya fitar a nanar juma’a, Kingibe ya ce baya da aniyar karawa da shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari, yayin da ya bayyana gamsuwa da salon mulkin shugaban na Najeriya.

Harkokin siyasa sun fada cikin hali na rashin tabbas a kasar, tun bayan da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya fito fili ya soki Muhammadu Buhari da salon shugabancinsa, kana ya bukace shi da kada ya nemi tsayawa takara a babban zaben kasar mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.