Taron Kwamitin tattauna samar da kudin ECOWAS na bai-daya

Shugabannin kasashen Afirka ta Yamma da ke cikin kwamitin tabbatar da aiwatar da amfani da kudin bai-daya sun gudanar da wani taro ranar Talata a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar. Shugabannin na fatar samar da kudin na bai-daya daga nan zuwa shekarar 2020.

An gudanar da taron ne da nufin samar da kudin bai-daya tsakanin kasashen ECOWAS

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na cikin kwamitin shugabannin kasashen da ke tattauna kudirin samar da kudin

An gudanar da taron ne karo na hudu tsakanin shugabannin kasashen na ECOWAS

Shugabannin na fatar cim ma manufar soma amfani da kudin a shekarar 2020.

Kwamitin ya kunshi shugabannin kasashen Kungiyar ECOWAS, sun hada da Nijar da Togo da Najeriya da Ghana

A 2014 aka kafa kwamitin da zai tattauna kudirin samar da kudin na ECOWAS

Karon farko ke nan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci taron.